23/11/2016
CIGABA DA TSARE SHAIKH ZAKZAKY YA SABAWA DOKAR KASA- Kungiyar CEDRA
* Gwamnati ta Sake Shi
*’Yan Jaridu s**a rika yiwa ‘Yan Shi’a adalci
Daga Mahdi Garba
Wata kungiya mai rajin kare hakkin bil adama mai suna ‘centrum initiative for development and fundamental rights advocacy (CEDRA) a turance, tayi kira da a saki jagoran harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibrahim Zakzaky. Tayi wannan kiran ne ranar laraba 23 ga watan Nuwamba, 2016 a babban dakin taron Julius Berger dake Jami’ar Lagos, a birnin Lagos din Nijeriya. Kiran ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar Dakta John Danfulani, Malami kuma mai rajin kare hakkin ‘dan Adam.
A gabatar da makasudin zuwanshi birnin Ikko don karanta kasidar tasa yace “na fito ne yau don tattauna yadda Gwamnati ke take hakkin ‘Yan Shi’a a wasu jihohin Arewacin Kasar. Kuma don neman goyon bayan masu fito-na-fito da zalunci a kudancin Kasar da ma duniya baki daya don irin yadda Gwamnatin Nijeriya da ‘yan amshin shatanta ke gasa musu dankali a hannu.”
Ya cigaba da cewa “a lokacin da Sojoji s**a je gidan Shugaban ‘yan Shi’a Shaikh Zakzaky a watan Disamban shekarar da ta gabata, fitowarsu kai kace fagen daga zasu je fafatawa da wani babban makiyi. Daga bisani s**a daukeshi zuwa wani wajen da babu wanda ya sani, kafin s**a mika shi ga jami’an tsaron farin kaya (DSS). Tun daga nan basu saken barinshi ya more ‘yancinshi da dokar Kasa ta 1999 ta tanadar ba don ko Kotu basu kaishi ba.”
Duk da fitowar da almajiransa suke don gabatar da muzaharar lumanan neman sakin Malaminsu a Abuja, Gwamnati tayi kunnen uwar shegu da bukatarsu. Malamin ya shigar da kara akan take mishi hakki da Gwamnatin tarayya take, wanda muna fatan zasu sakeshi da gaggawa don zuwa ganin likita da kuma more ‘yancinsa a matsayin ‘dan Adam” inji Dakta John Danfulani.
Da yake magana kan soke harkar da wasu Gwamnoni suke a fadin Kasar, yace “ wani abin da yake ci min tuwo a kwarya shine, a daidai lokacin da ‘yan harkar suke muzaharorin lumana don neman sakin jagoransu kamar yadda dokar kasa ta tanadar, kwatsam sai ga Gwamnonin wasu jihohin Nijeriya sun fara soke Harkar a jhohinsu, wanda haka katsalanda ne ga dokar Kasa. Saboda dokar Kasa ta baiwa kowanne ‘dan Kasa hurumin bautawa duk abinda ya yarda da shi.”
Ya kara da cewa “soke harkar a jihohin ne ya budewa wasu ‘yan jagaliya daman aukawa ‘ya ‘yan harkar a garuruwa daban-daban. Amma abin takaici babu wanda Gwamnati ta gurfanar a Kotu ya zuwa yanzu.”
Da yake korafi da nuna alhini akan rahotannin da ‘yan jarida suke kawowa duk lokacin da wani abu ya faru tsakanin ‘yan harkar da mahukuntan Kasar, ya yace “ a duk lokacin da aka yiwa ‘yan shi’a katsalanda akan ‘yancinsu, sai manema labarai su kawo wasu labarai masu ban dariya akan wai anyi fito-na-fito da Jami’an Soji ko ‘Yan Sanda. Wanda hakan ya tallafawa tatsuniyoyin da Gwamnati take yi ne akan ‘yan harkar na tafiya da muggan makamai a lokutan tarukansu. Wannan kawai labarin kanzon kurege ne.
Dakta Danfulani ya cigaba da koke akan dabi’ar wasu ‘yan jaridu da kuma gidajen Jaridun Kasar. Ya nuna takaici akan yadda ake shirya labaran karya akan ‘Yan IMN din, kuma idan s**a rubuta martini sai a jingine. Mafi munin lamari shine manyan gidajen jaridun Kasar basa son karban tallace-tallacensu.” Inji Shi.
Dakta Danfulani ya cigaba da cewa “yan jaridu suna daga cikin kashin bayan Dimokradiyya. Don haka idan ana son Dimokradiyya ya daure a kowacce Kasa dole a yiwa kowanne ‘dan Kasa adalci wajen kowa labarinsa.”
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan dabi’un Jakadun wasu manya kasashe da wasu kungiyoyi masu zaman kansu dake Nijeriya, yace “Jakadun wasu kasashe da wasu kungiyoyi masu zaman kansu su ma sun fada tarkon irin labaran da jaridun Nijeriya suke kawo kan lamarin”. Yace abin takaici shine yadda su ma suke ganin hare-haren a matsayin arangama. Yace “da Kafata naje tattakin arba’een na Kano don naga wainar da ake toyawa a wajen. Babu wani mai makami acikinsu, amma idan aka kawo musu hari sai ace arangama akayi”.
Idan ni daba ‘dan Shia ba, zan iya zuwa Kano mai zai hana Jakadun Amurka da sauran Kasashe zuwa wajen don cire kwarkwatar idanunsu?” ya karkare.