29/08/2022
Bayan ya Kira ta ta waya ya ce Mata qarfe 11:00 na dare zai iso gida Kuma ta ajiye Masa abinci, a wannan lokacin ne ta yanke shawarar cewa lallai a wannan dare za ta kashe shi. Ta tashi ta hada Masa abinci wajen kala 3 sannan ta hada masa jus Shima wajen kala 3, ta qawata teburin cin abincin da kyandir, ta zo ta zuba wata guba Mai qarfi a cikin kowane abinci da jus.
Wajen qarfe 12 ta ji Mai gadi ya bude get alamar Maigida ya dawo. Ta tashi ta tarbe shi bayan ya shigo. Ta CE Masa ga Abinci, ya CE sai yayi wanka sannan ya ci abincin.
Ya fito daga Wanka kawai sai yaga an banko qofar dakinsa, wasu qatti su 8 s**a banko dakin sun shaqo matar, kowanne da pistol, fuskokinsu ba annuri, Kai daga ganinsu ka ga emissaries of Death. Babban su ya ce tun airport muke binka, jakar da ka taho da ita muke son ka bamu ko Kuma mu kashe kyakkyawar matar Nan taka k**ar yadda muka kashe maigadinka.
Hankalin Maigidan Nan ya tashi saboda cikin jakar Nan gabadaya Arziqin sa na Duniya ne, akwai kudi sun Kai miliyan 330 a ciki, Amma Kuma sai ya Yi tunanin rayuwar Amaryarsa ta fi duk wata dukiyar da zai tara, bai yi watawata ba ya basu jakar s**a qyalesu bayan sun daure su. Za su fita sai s**a ga dining table cike da kayan ciye-ciye da shaye shaye, ai ba shawara kawai s**a hau abincin Nan da ci, s**a yi hani'an sannan s**a Kora Ruwan lemo sai s**a fara murde-murde, cikin mintina 5 s**a sheqa barzahu. Nan take matar ta fara kuka tana neman tuba wajen mijin. Ta fada Masa cewa ita ta zuba guba don ta kashe shi Amma Allah ya juyar da abun zuwa wani lamarin.